Sani Danlami ne kawai nake shakku domin yafini kyautatawa Al'umma ~ cewar Abokin Takarar Sani Danlami na Jam'iyyar adawa

 NAKAN RASA SUKUNI IDAN NATUNA CEWA DA SANI DANLAMI NIKE TAKARAR BANA ~ SUBUL-DABAKAN ABOKIN TAKARAR DANLAMI NA JAM'IYYAR ADAWA KENAN!!! 


18th Jan, 2023

Lawal Isah Federal 

Lawalisah95@gmail.com


 Dayawa daga cikin Abokanan Takarar Hon. Sani Aliyu Danlami (Me Raba Alheri) nata bayyana kalaman karaya karara, inda wasu ke kokarin yimasa kage wasu kuma sharri wasuma karya da shachi fadi, ana haka, kwatsam wani daga cikin Abokan Takarar tasa dake Jam'iyyar adawa yayi subul-dabaka cewa "nakan rasa sukuni a duk lokachin da natuna cewa da Sani Danlami nikeyin takara a bana, domin yanda sunansa ya karade gari cewa Me Raba Alherin dai".

 Wannan dan takara yayi wannan furuchi cikin gigicewa tareda karaya da Sani Danlami a wannan zabe me zuwa na 2023.


 Shidai Hon. Sani Aliyu Danlami ta raba Alherin sa yake akoda yaushe, baya waiwaye ga makiya ko mahassada, hasalima ko raddi bayayi ga wanda yaimasa sharri, ya fawwala komai nasa ga Allah SWA domin shike bada Mulki ga wanda yaso.

 Ina mai tabbatar ma Al'umma cewa, Wallahi Katsina Central tayi babban kamu samun Hon. Sani Aliyu Danlami (Garkuwan Arewa) a matsayin wakili, domin daga cikin sauran Abokanan Takararsa, shine wanda yasan wace unguwa ke bukatar Asibiti ko hanya, shine wanda yasan lungu da sakon mazabunnan, shine wanda idan ka ajesa daga Kofar Soro zai iya kaika kowace unguwa cikin garin Katsina batare da dan Kwatanceba ko direba. Kuzo muyi Hon. Sani Aliyu Danlami da alheri domin samun alherai daga me raba alheri.


Lawal Isah Federal, DG The Danlami Organization (TDO)


Comments

Popular posts from this blog

Dan-Lawan Katsina commiserates with Nigerians @ 14th remembrance of late Yar'adua

KTSG plans 1-Day masterclass program with Students leaders of the institutions of the state Katsina.

Dan-Lawan Katsina vows to retire in contesting any elective Political office as He'll be participating in Politics till last breath.