Nafi jindadi da samun natsuwa idan ina cikin Al'ummarmu, shiyasa ban canja Kasa ko Gari ba bayan nagama Majalissa ~ Hon. Sani Aliyu Danlami
BAN CANJA KASA KO GARI BA BAYAN NAGAMA MAJALISSA, INA ZAUNE NE CIKIN AL'UMMATA DOMIN BANDA INDA YAFINAN ~ Cewar Hon. Sani Aliyu Danlami (Me-Raba Alheri).
21st Nov, 2022
Lawal Isah Federal
Lawalisah95@gmail.com
Tun bayanda wa'adin wakilchina yakare a Majalissar wakilai dake babban birnin tarayyar Najeriya π³π¬ Habuja a matsayin dan Majalissa me wakiltar karamar hukumar Katsina, tunanin canja Kasa ko Gari bai zominba kamar yanda wasu keyi, ina zaune ne inda nasaba cikin 'Yan uwa da Abokan arzuki domin banda inda yafinan, hasalima dakaga nai Sati-daya bana Gida, to natai Umara ne ko harkokin kasuwanchi na.
Soyayyar Jiharmu da Al'ummarta sun cika zukatanmu, domin akoda yaushe tunaninmu idan Allah SWA yabamu wannan wakilchin taya zamu sauke wannan nauyi ta fuskar gina Al'umma dama Kasa baki daya.
Insha Allah zamu bada mamaki, inda zamu sake ba bangaren Ilimi muhimmanchi kamar yanda muke kamantawa yanzu haka duk da bamuda Kujera (Shirin Hasken Makaranta), zamu inganta fannin Lafiya a wannan yanki tareda samarda gine-gine masu inganchi domin habakar lafiyar Al'ummaru (ku mu leka Asibitin Rafin Dadi, shiya gyarata), maganar shige da fice wajen samarda ayyukanyi da sana'o'i ga Matasa, insha Allahu Rabbi za'a gani a kasa ba labari ba.
Al'ummar karamar hukumar Katsina, kumuzo musake ba Hon. Sani Aliyu Danlami (Garkuwan Arewa) dama a wannan kakar zabe me zuwa ta 2023 a Jam'iyyar APC me alamar Tsintsiya, domin shi yasan lungu da sako na yankunanmu, shiyasan ina ke bukatar Kwata ko Hanya, shiyasan ina ke bukatar Jari ko Offer, domin shike zaune cikinmu duk wuya duk runtsi, kai ko lokachin Korona ma yananan Gida Katsina inda samar da Abinchi yazama aikinsa Dare da Rana. Allah yabamu sa'a yai mamu Jagoranchi ameen.
#MeRabaAlherinMukeyi
#MunaAPCnDai
Activist Lawal Isah Federal.
Comments
Post a Comment