Zanyi nazari sosai akan Suratul Yusufa domin akwai Ilimin magance Matsalar yunwa acikinta ~ cewar Hon. Aminu Chindo.

 Da masu madafun iko zasu koma akan Al-kitabu was Sunna (watau tsayuwa akan Littafin Allah da Sunnonin Annabi SAW da yanda Sahabbai sukai Rayuwarsu), to da sunyi Mulkinsu cikin salama kamar yanda Annabi Yusuf (AS) yayi sanda yana Sarki.


 An fuskanchi lalurar Yunwa lokachin Annabi Yusuf (AS), wanda kasancewarsa na Annabin Allah, yayi dubaru sosai domin kaucewa wannan Matsala ta yunwa wanda daga bisani yayi nasara akanta, idan Al-ummar Karamar Hukumar Katsina suka bamu damar wakiltarsu a Majalissar wakilai, insha Allahu Rabbi zamuyi koyi da Annabawa da Sahabbai wajen wakiltarsu da kwatanta adalchi, haka zalika, zamubi hanyoyin da sukabi wajen magance Annobobin da akai a zamaninsu wajen magance namu matsalolin na wannan karni.


 Hon. Aminu Ahmadu Chindo yakarawa dacewa, ya inganta Al-ummar Musulmi mutashi tsaye musamman acikin wannan wata na Haihuwar 'Dan gata Muhammadu Rasulillahi SAW wajen rokon Allah SWA daya magance mamu matsalolin damuke fuskanta musammanma a bangaren Tsaro, tattalin arziki da yanda aka maida harkar Ilimi da nemansa koma baya domin Allah me jinkan bayinsa ne. 

 Daga naku watau, Hon. Aminu Ahmadu Chindo 'Dan Takarar Majalissar wakilai me wakiltar Karamar Hukumar Katsina a karkashin Jam'iyyar PDP me alamar Lema. 


Activist Lawal Isah Federal, Shugaban Kungiyar Chindo Support Organization (CSO).


Comments

Popular posts from this blog

Dan-Lawan Katsina commiserates with Nigerians @ 14th remembrance of late Yar'adua

KTSG plans 1-Day masterclass program with Students leaders of the institutions of the state Katsina.

Dan-Lawan Katsina vows to retire in contesting any elective Political office as He'll be participating in Politics till last breath.