DAN-LAWAN KATSINA NE YAFI CHANCHANTA YAZAMA DAN MAJALISSAR DATTAWA A KATSINA TA TSAKIYA ABISA DALILAI KAMAR HAKA..!

DAN-LAWAN KATSINA, HON. HAMISU GAMBO NE YAFI CHANCHANTA YAZAMA DAN MAJALISSAR DATTAWA A KATSINA TA TSAKIYA ABISA DALILAI KAMAR HAKA..! 



12th May, 2022

Lawal Isah Federal 

Lawalisah95@gmail.com


Bismillahi,

Atakaiche, idan kafara duba batun nasaba, watau Hon. Hamisu Gambo (Dan-Lawan Katsina) 'dan dangi ne daga babban Gida a cikin birnin Katsina, sannan mutum ne me ilimin Muhammadiyya me zurfin gaske gakuma ilimin Zamani gaya, mutum ne daya zauna da magabata sau da kafa irinsu me martaba marigayi Kabir Usman (wanda shine yabasa Sarautar Dan-Lawan Katsina), irinsu marigayi Mal. Umaru Musa Yar'adua dadai sauransu, shiyasa dayawan halayensa suke kamanche-cheniya. 


 Idan kazo ta fuskar gina Al'umma da chigaban Kasa,  Hon. Hamisu Gambo shine mutuminda yafara bada wurin kebe masu lalurar Covid-19 a Jihar Katsina (Isolation Center), sannan ya gina Makarantu tun daga matakin Nursery, Primary, Secondary, School of Health Technology, School of Higher Studies affiliated to ABU, College of Agriculture, Vocational Training College dadai sauransu, sannan yasamar da Asibiti me akalla Gado Dari. Watau abubuwan da yawa wanda har yanzu Jama'a na chin gajiyarsu a Jihar Katsina.


Sanda yayi Dan Majalissar Wakilai, yasamarwa Matasa ayyukan yi musamman Aikin Sulke (Force), wanda Dalibai saida suka zama 'Yan gata domin Scholarship ba kama hannun yaro, Fanfunan Tuka-tuka da kwatochi yayi su dayawa wanda yanzu haka wasu daga cikin Fanfunan na Aiki, Jari kuwa ga masu manya da matsakaitan Sana'o'i sai alasam barka, idan abun jaje ko murna yasamu to yana gaba-gaba wajen taya murna ko jajantawa wanda har yanzu halinsa kenan.

 

Sanda yana shugaban karamar Hukumar Mulki ta Katsina, duk watan Duniya saiya raba kayan masarufi ga Al'umma, sannan duk wata mazaba (ward) dakeda wata bukata madamar batunta yazomai tofa matsalar ta kare. SHINE WANDA ya yanka filayen babbar Kasuwar Katsina (Central Market) amma ko shago daya bai dauka ba kuma baya dashi achen har zuwa yanzu (watau amanarsa takai kololuwa).


 Dalilan suna da yawa wallahi, sabili da haka ne yasa nace shine yafi chanchanta ya dare a wannan Kujera ta 'Dan Majalissar Dattawa me wakiltar Katsina ta tsakiya a kakar zabe me zuwa ta 2023 a karkashin Jam'iyyar PDP me alamar Lema ☂.

 Dafatan Allah SWA yabashi nasara yakuma yimasa jagoranchi akai idan ya samu, ameen. 


Activist Lawal Isah (Federal).

Comments

Popular posts from this blog

Dan-Lawan Katsina commiserates with Nigerians @ 14th remembrance of late Yar'adua

The Man Sani Danlami presides presentation of letter of provisional appointment to GIAL Academic Staff

Sadeeq Dan-Lawan weds Hauwa'u Muh'd just from seeking parental permission at Engr. Buba Galadima's resistance Abuja