Jaridar Peoples Reporter zata dawo aiki gadan-gadan

 Jaridar Peoples Reporter mallakin Hon. Hamisu Gambo (Dan-Lawan Katsina) zata dawo aiki gadan-gadan


 Biyo bayan gyare-gyaren da kamfanin Jaridar Peoples Reporter yayi na daidaita jaridar daidai da zamani domin masu karatu, me girma Hon. Dan-Lawan Katsina nawa Al'umma albishiri cewa Jaridar zata dawo aiki gadan-gadan cikin 'yan lokuttan nan


 Jaridar Peoples Reporter tayi zarra wajen kawo labaru sahihai tareda tsayuwa kan gaskiya, haka zalika ma'aikatan wannan Jarida kwararrune wajen aikinsu. Jaridar Peoples Reporter tasamu lambobin yabo daga manazarta daban-daban.


 Hon. Hamisu Gambo (Dan-Lawan Katsina) shine mamallakin wannan Jarida ta Peoples Reporter, sannan yabada umarnin chigaba da ayyuka bayan hutun shekara 5 da Jaridar tayi abisa wasu gyare-gyare da tayi na fadada ayyukan Jaridar.


 Yanzu haka dai wannan Kamfani ya shirya tsaf domin chigaba da ayyukansa. 'Yan team na wannan Jarida ta Peoples Reporter sun hada da; Ambrose Sule, Abdul Azeez, Aminu Yusuf, Living Stone, Florence Udo, Lucy Johnson, Emeka Kalu, Abubakar Shuaibu, Adjara Ahmedu da Lawal Isah,  sai shugaban wannan Kamfani Hon. Hamisu Gambo (Dan-Lawan Katsina).


Comments

Popular posts from this blog

Dan-Lawan Katsina commiserates with Nigerians @ 14th remembrance of late Yar'adua

The Man Sani Danlami presides presentation of letter of provisional appointment to GIAL Academic Staff

Sadeeq Dan-Lawan weds Hauwa'u Muh'd just from seeking parental permission at Engr. Buba Galadima's resistance Abuja