Duk me sunan Dikko yanada Tarihin rikon Amana da gaskia, don haka Katsinan Dikko ta Dikko ce ~ Inji Dan-Lawan Katsina.

 JIHAR KATSINA NA BUKATAR HAZIKIN MATASHI ME ILIMIN ADDINI DANA ZAMANI YA GAJI GWOMNA MASARI, DON HAKA KATSINAN DIKKO TA DIKKO CE ~ INJI DAN-LAWAN KATSINA.


20th Dec, 2022

Lawal Isah Federal 

Lawalisah95@gmail.com


 Jim kadan bayan kammaluwar yakin neman zaben Dan takarar Gwomnan Jihar Katsina a Jam'iyyar APC me albarka watau Dr. Dikko Umaru Radda a shiyyar Katsina ta Arewa (Daura Zone) inda aka rufe da karamar hukumar Kankia, me girma Gwomnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari (Matawallen  Hausa, Dallatun Katsina) yasamu halarta tareda tawagarsa inda daya daga cikin Sojin wannan tafiya watau Hon. Hamisu Gambo (Dan-Lawan Katsina) yayi sharhi akan wanda Al'ummar Jihar Katsina yakamata su zaba a wannan kakar zabe ta 2023


 A lokachin bayaninsa yace, Jihar Katsina na bukatar wanda zai gaji me girma Gwomna Masari yazamto hazikin Matashi wanda keda Ilimin Muhammadiyya dana Zamani, kuma wayayye wanda baida Tarihin chin Amana ko zamba, shiyasa Dr. Dikko Umaru Radda yazama Dan Takarar Jam'iyyar ta APC saboda yanada wadannan kamalu da Jihar ke bukata duk da cewa ita dai Jihar Katsinan Dikko, aita Dikko ce.


Me girma Dan-Lawan Katsina, Hon. Hamisu Gambo yakara da cewa, yakamata mufito dukkanmu domin jefa Kuru'unmu ga Yan takarkarun Jam'iyyar APC daga kasa har sama domin daurewar chigaba da tattalin arziki, saboda idan akai duba Yan Takarar Jam'iyyar APC kaso 75 nasu sunfi na saura Jam'iyyun chanchanta da Tarihi me kyau.

 Allah SWA yabamu sa'a ameen.


Lawal Isah Federal, press Secretary to Hon. Hamisu Gambo (Dan-Lawan Katsina)


Comments

Popular posts from this blog

Dan-Lawan Katsina commiserates with Nigerians @ 14th remembrance of late Yar'adua

KTSG plans 1-Day masterclass program with Students leaders of the institutions of the state Katsina.

Dan-Lawan Katsina vows to retire in contesting any elective Political office as He'll be participating in Politics till last breath.