An gudanar da gagarumin taro na Kungiyar "Rahamawa/Sokoto Rima Women Development" domin jaddada goyon bayan Kungiyar ga Hon. Aminu Chindo.


 Da yammachin yau Lahadi ne me girma 'Dan Takarar Majalissar wakilai me wakiltar Karamar Hukumar Katsina ta tsakiya ya halarchi gagarumin taron kungiyar "Rahamawa/Sokoto Rima Women Development" data shirya domin nuna goyon baya da alkawarin Kuru'unsu garesa a wannan zabe da muke tunkara na 2023.


 Ta bakin shugabar kungiyar Hajia Jummai a madadin sauran Mata tasha alwashin kawo kuru'unsu kaf domin samun nasarar Jam'iyyar PDP me alamar lema. 

 Hajia Jummai dai ta kara da cewa, a wannan yanki nasu sunyi dan majalissa haka zalika har kwamishina yayi amma shiru kakeji, basusan wani dadin dimokaradiyyarsa ba bayan kuma su suka kaishi. Daga karshe Hajia Jummai ta rufe da addu'ar neman sa'a ga Hon. Aminu Ahmadu Chindo. 


Ta bakin 'Dan takarar watau Hon. Aminu Chindo, yafara da godewa Allah SWA daya hada fuskokinshi dana masoyanshi a dai-dai wannan lokachi, sannan ya chigaba da bayanin godia ga daukachin wadannan Mata da shuwagabanninsu tareda jinjina masu akan hada wannan gagarumin taro. 

 Daga karshe Hon. Aminu Chindo ya tabbatar masu da rike amanarsu tareda wakiltar yanda yadace idan Allah yakaisa ga nasara akan wannan, sannan yayi kira garesu dasu zabi Jam'iyyar PDP daga sama har kasa haka zalika daga kasa har sama. 


Activist Lawal Isah Federal for CSO

Comments

Popular posts from this blog

Dan-Lawan Katsina commiserates with Nigerians @ 14th remembrance of late Yar'adua

KTSG plans 1-Day masterclass program with Students leaders of the institutions of the state Katsina.

Dan-Lawan Katsina vows to retire in contesting any elective Political office as He'll be participating in Politics till last breath.