Zanyi nazari sosai akan Suratul Yusufa domin akwai Ilimin magance Matsalar yunwa acikinta ~ cewar Hon. Aminu Chindo.
Da masu madafun iko zasu koma akan Al-kitabu was Sunna (watau tsayuwa akan Littafin Allah da Sunnonin Annabi SAW da yanda Sahabbai sukai Rayuwarsu), to da sunyi Mulkinsu cikin salama kamar yanda Annabi Yusuf (AS) yayi sanda yana Sarki. An fuskanchi lalurar Yunwa lokachin Annabi Yusuf (AS), wanda kasancewarsa na Annabin Allah, yayi dubaru sosai domin kaucewa wannan Matsala ta yunwa wanda daga bisani yayi nasara akanta, idan Al-ummar Karamar Hukumar Katsina suka bamu damar wakiltarsu a Majalissar wakilai, insha Allahu Rabbi zamuyi koyi da Annabawa da Sahabbai wajen wakiltarsu da kwatanta adalchi, haka zalika, zamubi hanyoyin da sukabi wajen magance Annobobin da akai a zamaninsu wajen magance namu matsalolin na wannan karni. Hon. Aminu Ahmadu Chindo yakarawa dacewa, ya inganta Al-ummar Musulmi mutashi tsaye musamman acikin wannan wata na Haihuwar 'Dan gata Muhammadu Rasulillahi SAW wajen rokon Allah SWA daya magance mamu matsalolin damuke fuskanta musammanma a bangaren Ts...